Tsohon alkalin babbar kotun jihar Kano mai shari’a Wada Rano ya rasu

WhatsApp Image 2025 04 17 at 13.47.38 720x430

Tsohon alkalin babbar kotun jihar Kano mai shari’a Wada Umar Rano ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.

Marigayi Rano, wanda ya yi ritaya a shekarar 2013, ya rasu ne a ranar Alhamis da misalin karfe 11:20 na safe a asibiti sakamakon rashin lafiya, kamar yadda babban dansa Umar Wada Umar Rano ya tabbatar wa SolaceBase.

Umar ya ce za a yi sallar jana’izar mahaifinsa da misalin karfe 3:00 na rana a yau a gidansa na Sharada, kusa da hedikwatar hukumar Hisba.

Ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya da dama, da jikoki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here