Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta mayar da martani kan rade-radin da ake ta yadawa dangane da ficewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban NNPP zuwa APC.
Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar a Kano ranar Juma’a, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya tabbatar da cewa, jam’iyyar APC a karkashin sabon tsarinta, na karbar sauye-sauye daga jam’iyyun siyasa daban-daban.
SolaceBase ta rawaito cewa jam’iyyar ta nuna damuwa kan abin da ta kira dabarar kokarin da wasu ‘yan siyasa musamman wadanda ke fuskantar rigima a jam’iyyun su ke yi na neman mafaka a cikin APC.
Ya kuma kara jaddada cewa shiga jam’iyyar APC ba garkuwa ba ce daga binciken cin hanci da rashawa ko kuma illar cin hanci da rashawa, musamman daga hukumomi irin su EFCC da ICPC.
Karin karatu: Da ɗumi-ɗumi: Kawu Sumaila, Ali Madaki, Rurum da sauran jiga-jigan NNPP sun gana da Ganduje kafin komawa APC
Jam’iyyar ta bukaci duk wani tsohon jigon siyasa musamman wadanda a baya suka yi kalaman batanci ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, su nemi gafarar jama’a domin nuna nadama da mutuntawa.
Jam’iyyar APC ta Kano ta jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma tsarin siyasa na gaskiya, inda ta bukaci masu son shiga jam’iyyar da su dace da tsarin jam’iyyar maimakon amfani da ita a matsayin hanyar tsira.