‘Yan bindiga sun kashe 3, sun kone gidaje a Neja – ‘Yan Sanda

bandits 1 750x430 (1)

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga da ake zargi sun kashe mutane 3 a kauyen Pissa da ke Karamar Hukumar Borgu

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Asabar cewa ‘yan bindigar sun kai hari kauyen da misalin karfe 9:00 na safe.

Ya ce an ƙone wasu gidaje yayin harin, duk da haka ya kara da cewa sojoji sun fafata da‘yan bindigar, amma ba a fitar da cikakkun bayanai kan arangamar ba a yanzu.

“Rahoton da muka samu ya nuna cewa ‘yan bindiga da ake zargi sun mamaye kauyen Pissa da ke Karamar Hukumar Borgu.

“An ce an kashe mutane 3 yayin harin, kuma an kone wasu gidaje.

“Duk da haka, sojoji sun amsa kiran sun fuskanci ‘yan ta’addan, amma babu wani karin bayani kan yadda ta kasance da su har yanzu,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here