Biyo bayan kisan gilla da ‘yan dindiga suka yi wa sama da mutane tamanin a Karamar Hukumar Sabon Birnin dake jihar Sokoto, shugabannin Karamar Hukumar sun rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika domin kokawa game da irin kisan gillar da ake yi wa al’ummominsu.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yan bindigar sun tare wata motar ‘yan ci-rani a kauyen Gidan Bawa da ke Sokoto, inda suka kona fasinjoji sama da 40 kurmus.
A cikin wasikar, shugabannin Karamar Hukumar Sabon Birnin sun shaida wa Buhari cewa, sun kadu da irin kisan da ake yi wa jama’arsu musamman a yankunan Isa da Sabon Birni da Goronyo da kuma Karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara mai makwabtaka da Sokoto.
Wasikar ta ce, ‘yan ta’adda masu biyayya ga kasungurmin dan bindigar nan, Bello Turji na kai farmaki kan al’ummomin wadannan wurare, inda suke yi wa mata fyade ba ya ga lalata kadarori da dukiyoyin jama’a.
Ko a can baya, jama’ar Sabon Birnin sun taba rubuta wa shugaba Buhari wasika domin shaida masa irin ukubar da suke fuskanta a yankinsu a dalilin hare-haren ‘yan bindiga.













































