Yan bindiga sun kashe yan sanda hudu ranar Litinin a karamar hukumar Bunguda dake karamar hukumar Zamfara.
Yan bindigar sun farmaki yan sandan ne ya yin da suke kan aiki a wajan shingin binkice.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata da safe.
Sai dai bai tabbatar da cewa ko yan sandan sun mutu nan take yayin harin ba, amma ya yi alkawarin zai yi karin bayani a nan gaba.