Ma’aikatan lantarki a karkashin inuwar Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa, (wato NUEE), sun bawa mahukuntan Kamfanin rarraba wutar lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Kuma Katsina wato KEDCO, wa’adin kwanaki 14 kan ya biya su kudadensu da ake yanka da nufin Sanya musu a asusun Fansho Amma ba a Sanya musu, ko su tsunduma yajin aiki.
Ma’aikatan sun yi barazanar gurgunta ayyukan kamfanin da ake rabawa idan har kamfanin ya kasa yin abin da ya dace.
Jaridar Solacebase ta tawaito cewa a cikin wata takardar korafi da ya aike ta ga Manajan Darakta na kamfanin da kuma kwafinta ga Darakta-Janar na kamfanin da Daraktan Hukumar, DSS, da Babban Sakataren Kungiyar NUEE, a madadin ma’aikatan, Joe Ajaero, ya koka bisa yadda ake ci gaba da cire musu kudade ba tare da shigar musu ba, da kuma rashin girmama yarjejeniyoyin da aka cimma da kungiyar kan wannan batu da sauran batutuwan da suka shafi mataimakan.

Ya kara da cewa kungiyar ta kafa kwamitin da zai rinka bin diddigin biyan bashin a KEDCO wanda ya ba da shawarar tsarin biyan kudi a cikin watanni hudu, ya mika rahotonsa a wata takarda mai kwanan wata 21 ga watan Janairu, 2022, yana mai cewa: “A wani taro da aka yi a ranar 30 ga watan Maris din Shekarar 2022 tsakanin kungiyar da kuma mahukunta kamfanin na KEDCO akan jinkiri wajen aiwatar da rahoton kwamitin da aka bayyana a sama tare da inganta abubuwan da suka shafi gudanarwar, da Kuma cika alkawarin fara biyan kudi ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai abin takaicin shi ne, ba a biya kudaden ba, da sauran batutuwan da suka shafi ma’aikata har yau.













































