Shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, Dr. Sidie Tunis, ya bada umarnin dakatar da daukar ma’aikata ba tare da bata lokaci ba.
Ya kuma kafa wani kwamati da zai yi binkice kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi yayin gudanar da daukar ma’aikatan.
Tunis ya bada uamrnin ne a wata sanarwa da bangaran yada labarai na kungiyar ya fitar.
Dakatarwar ta biyo bayan zargin wakilan Najeriya a kungiyar da yin cushe yayin gudanar da daukar ma’aikatan da kungiyar ta fara.













































