Ku Aje Kamfe Mu Taimaka Wa Mutane, Peter Obi Ga Sauran Yan Takara

682494e5eb6449cb
682494e5eb6449cb

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi kira ga takwarorinsa su dakatar da yaƙin neman zaɓe kana su haɗa hannu da shi domin tallafawa mutanen da Ibtila’in Ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar nan.

Channels tv tace Mista Obi ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a gidansa dake Abuja.

Channels tv tace Mista Obi ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a gidansa dake Abuja.

Yayin ziyarar, Obi da gwamnan Ortom sun tattauna kan yadda zai kai ziyara wuraren da Ambaliyar ta shafa a jihar Benuwai dake Arewa ta tsakiya da sauran wasu jihohi.

Tsohon gwamnan Anambra na cikin masu tseren gaje Buhari tare da Bola Ahmed Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Rabiu Kwankwaso na NNPP da sauran su.

Obi yace yana tsammanin yan takarar shugaban ƙasan su nuna damuwarsu ga bayin Allah da Ibtila’in ya afka mawa idan aka yi la’akari da miliyoyin da suka ƙashe wajen sayen Fom ɗin takara. Legit.ng Hausa ta gano cewa matsalar Ambaliyar ruwa ta jawo asara da dama a sassan wasu jihohin Najeriya cikin watanni biyu da suka gabata.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce kusan mutane miliyan Biyu da rabi lamarin ya shafa yayin da Ambaliyar ta kashe mutum 603.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here