DA DUMI-DUMI: Kotu ta janye umarnin hana taron jam’iyyar APC na kasa

BREAKING
BREAKING

A ranar Juma’a ne wata babbar kotun birnin tarayya ta bayar da umarnin soke dokar hana taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Maris.

Kotun da mai shari’a Bello Kawu ya jagoranta ta ce dan jam’iyyar siyasa ba zai iya kai karar jam’iyyar ba.

Mai shari’a Kawu ya ce wa’adin ranar 18 ga watan Nuwamba, 2021, ya ci karo da hukuncin da kotun koli ta yanke kwanan nan kan wani lamari makamancin haka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here