Wani jirgin sama kirar Boeing 737 dauke da fasinjoji 132 ya yi hatsari a yankin Guangxi Zhuang dake kudancin kasar China, wanda kawo yanzu ba’a iya tantance adadin mutanen da abun ya rutsa dasu ba.
Jirgin mai lamba MU 5735 ya tashi ne daga filin jirgin sama na Changshui dake kudu maso yammacin China da misalin karfe daya da minti sha biyar na rana, inda aka tsara cewa zai sauka a filin jirgin sama na Guangzhou da misalin karfe biyar da minti bakwai.
Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka tura jami’an ceto wurin da lamarin ya faru, inda kawo yanzu hukumomi a kasar ta China basu ce komai kan lamarin ba.
Jirgin da ya yi hatsarin mallakin kamfanin Yunnan ne, wanda ya kasance karamin kamfani mallakin kamfanin jirgi na gabashin China.