Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta yanke wa wata mata, Halima Haliru Umar, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali bayan an same ta da laifin mallakar harsasai 302 masu rai na AK-47 ba bisa ka’ida ba da kuma kokarin bayar da tallafi don aikata ayyukan ta’addanci.
Wadda ake tuhuma ta amsa laifinta a ranar 11 ga Maris bayan da hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS)ta kamata a Jihar Filato, ta kuma gurfanar da ita gaban kotu kan kararraki biyu daga cikin hudu.
Bayan gurfanar da ita, an sake duba bayanan laifukan da ake tuhumar ta na uku da hudu, wadanda ta amsa, sannan Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta dage shari’ar domin yanke hukunci kan biyu da ta amsa.
A hukuncinta, Mai Shari’a Yilwa ta bayyana cewa wanda ake tuhuma ta amsa laifinta kan tuhuma ta uku da ta hudu daga cikin hudun a ranar da aka gurfanar da ita.
Mai shari’ar ta kara da cewa ta hanyar amsa laifinta, ta yarda da bayanan da masu shigar da kara suka gabatar, ba tare da gabatar da wata shaida a matsayin kare kanta ba.
Bayan yanke wa wanda ake tuhuma hukunci, lauyan dake kare ta, Hamza Dantani, ya roki kotun ta yi sassauci wajen yanke hukunci a kan wanda yake karewa.
Dantani ya ce wanda ake tuhuma bata taba aikata laifi ba a baya kuma ta yi nadama, ya kara da cewa ba ta bata lokacin kotu ba dangane da tuhume-tuhumen na uku da hudu.
Lauyan masu shigar da kara, Caliistus Eze, ya ce masu shigar da kara ba su da wani tarihin wanda ake tuhuma na an taba yanke mata hukunci a baya.
Mai Shari’a Yilwa, wacce ta dakatar da zama na dan lokaci, daga baya ta dawo ta bayyana hukuncinta ta hanyar yanke wa wanda ake tuhuma shekaru 20 kan tuhuma ta uku da shekara daya kan ta hudu.
Mai shari’a ta dage shari’ar zuwa 9 ga Yuli domin masu shigar da kara su fara shari’a kan tuhume-tuhume na daya da na biyu, wadanda wanda ake tuhuma ta musanta.












































