Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron koli na 69 na Hukumar Shugabannin Kasashe da Gwamnatocin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Freetown, babban birnin kasar Saliyo.
Ana sa ran Shettima zai hadu da sauran shugabannin yankin na Afirka ta Yamma a wani taron da za a gudanar a ranar Lahadi a Cibiyar Taro ta Duniya ta Julius Maada Bio.
A cewar wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman na Shugaban Kasa kan Harkokin Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Stanley Nkwocha ya fitar, taron zai duba muhimman shawarwari da kudirori, kuma ana sa ran shugabannin za su sake jaddada kudirin da suka dauka kan zaman lafiya, dimokuradiyya, ci gaban tattalin arziki da hadin kai a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa “Taron wani bangare ne na tarukan tsakiyar shekara na ECOWAS, wadanda yake hada shugabannin kasashe da gwamnatoci, ministoci, manyan jami’ai da hukumomin yankin domin duba ci gaban da aka samu a fannonin da kungiyar ta sa gaba da suka hada da tsaro, mulkin dimokuradiyya, kasuwanci, ababen more rayuwa da ci gaba mai dorewa.’’
Ana kuma sa ran taron zai karfafa hukumomin ECOWAS tare da inganta hadin gwiwa yayin da yankin ke fuskantar kalubalen siyasa, tattalin arziki da rashin tsaro da ke karuwa.
“Kafin taron shugabannin, kwamitin gudanarwa da kasafin kudi, kwamitin sulhu da tsaro da majalisar ministoci sun gana a Freetown domin nazarin batutuwan gudanarwa, kudi da na hukumomi kafin gabatar da shawarwari ga hukumar shugabannin kasashe da gwamnatoci.’’
A matsayin wani bangare na shirye-shirye, gwamnatin Saliyo ta kaddamar da Cibiyar Taro ta Duniya ta Julius Maada Bio da kuma wani rumbun adana kayayyaki na ECOWAS don tallafawa tarukan da kuma sauran harkokin kungiyar na gaba.













































