Shugabar kungiyar matan Kannywood ta Najeriya (K-WAN), Hauwa Bello, ta yi kira da a samar da hanyoyin inganta aiki da sauran damammaki ga mata masu shirya fina-finai a masana’antar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Kannywood ta kasance masana’antar wasan kwaikwayo na fina-finan Hausa.
Bello tayi wannan kiran ne a wata tattaunawa da ta yi da NAN a gurin taron horaswa da hukumar tace fina-finai ta kasa (NFVCB) ta shirya a zauren gidan talabijin na Kannywood da ke Kano.
Taron tattaunawa mai taken ‘NFVCB samu halartar masu shirya fina-finai, da suka hada da daraktoci, furodusoshi, masu daukar fina-finai, editoci, ’yan wasa da a cikin masana’antar.
Shugaban matan Kannywood ta shaida wa NAN cewa masana’antar fina-finan Hausa na da tarin jarumai mata da suka taka rawar gani, amma har yanzu ba su taka rawar gani ba a harkar shirya fim.













































