Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar SSANU da NASU za su fara yajin aiki na sai bana ta gani a daren Lahadi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi mai dauke da sa hannun shugaban SSANU na kasa, Mohammed Ibrahim, babban sakataren kungiyar ta NASU, Prince Peters Adeyemi, ta ce wa’adin da ta bai wa gwamnatin tarayya albashin da ta rike zai kare ne a ranar Lahadi da tsakar dare.
Kungiyoyin dai na neman a biya su albashin watanni hudu da aka hana su, a kara musu alawus alawus da kuma aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnati a shekarar 2009.