Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Najeriya, ta bayyana zargin cewa wasu daga cikin jami’anta na da ta’adar shirya wa ɗaurarru yadda za su kauce wa wa’adin da aka ɗibar musu, a matsayin rashin gaskiya, kuma abin takaici.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar Francis Enobore, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa wani lauya mai kare hakkin bil’adama Femi Falana, ya yi zargin cewa wasu jami’an hukumar na barin masu aikata laifuka su kubuta daga hukuncin da kotu ta yanke ta hanyar sa wasu su yi zaman gidan yari a madadin masu aikata laifukan.
“Yanzu ana tada jijiyar wuya game da shirye-shiryen jin ra’ayin jama’a na ci gaba da tsare mutane, banda wadanda aka yanke wa hukunci, amma duk da haka ba a ambaci sunayen mutane ko cibiyar tsare mutane da suke hakan ba.
“An tilastawa ma’aikatar ta mayar da martani ga wannan zargi domin gyara tunanin mutane da kuma kawar da rashin fahimtar bayanan da ka iya jefa rudani a zukatan ‘yan Najeriya.
“Don kaucewa shakku, game tsarin shigar da mutane gidan yari yana farawa ne daga kotu inda ake bayar da sammacin dake dauke da bayanan wanda abin ya shafa.” in ji shi.
Mai magana da yawun hukumar ya kuma ce Konturola Janar Haliru Nababa, ya mayar da hankali kan kula da fursunoni don kyautata rayuwarsu.
Babban Konturolan ya kuma ba da tabbacin kudurinsa na tsayawa tsayin daka wajen kai hukumar ga tudun mun tsira.













































