Jagoran jam’iyyar APC kuma mai ra’ayin takarar shugaban kasa a zaɓen baɗi Bola Tinubu, yana ganawa da mambobin kungiyar gwamnonin jam’iyyar sa’o’i kaɗan bayan da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar shugaban kasa.
Osinbajo ya bayyana sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a cikin wani faifan bidiyo a yau Litinin.
Solacebase ta ruwaito cewa kimanin gwamnonin APC 14 ne ke halartar taron.
Haka zalika taron yana gudana ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi, gwamnan Kebbi Atiku Bagudu kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC.













































