Hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar gwaji ta bana

JAMB Exam 678x381 1
JAMB Exam 678x381 1

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Najeriya JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar ta gwaji wadda ɗalibai suka rubuta ranar 9 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki.

JAMB ta bayyana haka ne a cikin sanarwar da take fitarwa mako-mako wadda ofishin magatakardar hukumar ya fitar yau Litinin a yau Abuja.

“Saboda haka, ɗaliban da suka yi rijista sai su ziyarci www.jamb.gov.ng su danna ‘2022 Mock Result Checking’ su shigar da lambar rajistar UTME don samun sakamakonsu,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa akalla dalibai 175,000 ne suka zana jarrabawar a cibiyoyin JAMB 757 a faɗin Najeriya.

Magatakardar hukumar Farfesa Is-haq Oloyede, wanda ya zanta da NAN bayan gudanar da atisayen a ranar Asabar, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake gudanar da atisayen.

Oloyede ya ce, ɗalibai 175,000 da suka rubuta jarabawar an takaita su ne kawai a zama daya wanda aka fara daga karfe 8 na safe zuwa karfe 10 na safe.

Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar da dukkan cibiyoyin na’urar kwamfuta CBT sun shirya don gudanar da babbar jarrabawar ta bana da ke tafe daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu.

Haka kuma NAN ta ruwaito cewa, an yiwa mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas rijista waɗanda za su rubuta babbar jarrabawar ta UTME a bana.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here