Babban Lauyan Najeriya, SAN, Femi Falana ya bayyana fatansa cewa za a janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke yi nan da kwanaki ba makonni ba.
Babban Lauyan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da littafi mai suna ‘Breaking Coconut With Your Head’ na Lanre Arogundade a yau Litinin a Legas.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar a janye yajin aikin a wajen kotun, inji jaridar Tribune.