Ba Mu Hana Dalibai ‘Yan Kasa Da Shekara 18 Rubuta Jarrabawar WASSCE, NECO Ba – Minista

Minister of State for Education Dr Yusuf Sununu 750x430

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi karin haske kan cewa ma’aikatar ba ta hana daliban da ba su kai shekara 18 ba rubuta jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) da Jarrabawar ta NECO.

Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a yayin da yake ansa tambayoyi daga ‘yan jarida a wani taron tunawa da ranar karatu ta duniya ta 2024 (ILD).

Sununu ya ce rashin fahimtar da jama’a suka yi da kuma fahimtar da Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya yi abu ne mai matukar takaici.
Ya ce a zahiri ministan yana magana ne kan shekaru 18 na shiga manyan makarantu kamar yadda aka yi a tsarin ilimi na 6: 3: 3: 4.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here