Tinubu Ya Amince da murabus din mai magana da yawun sa

IMG 20240621 WA0000 678x430 1

Shugaba Bola Tinubu ya amshi takardar daga Ajuri Ngelale, mai magana da yawunsa kuma wakilin shugaban kasa na musamman kan harkokin sauyin yanayi, inda ya sanar da shi murabus dinsa saboda wasu dalilai na kashin kansa da kuma lafiya.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Asabar ta ce shugaban ya amince da dalilan Ngelale na murabus din.

Yayin da yake mika addu’o’insa da fatan alheri ga Ngelale da iyalansa, shugaban ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa.

Ya lura da kokarin Ngelale da sadaukarwa wajen yi wa al’umma hidima, ya kuma gode masa bisa gudunmawar da ya bayar, musamman wajen bada jawabai na kasa gaba daya da kuma jagorantar kokarin da ake yi kan ayyukan sauyin yanayi da sauran muhimman tsare-tsare.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here