Kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara aiwatar da sabon tsarin Dual Mandate Policy a dukkan kwalejojin ilimi na ƙasar nan, wanda ke ƙunshe cikin sabuwar dokar kwalejojin ilimi ta 2023.

A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar ilimi mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar Folasade Boriowo, inda ta bayyana cewa dokar ta bai wa dukkan kwalejojin damar bayar da shaidar karatu ns digiri da kuma NCE a lokaci guda a fannin koyarwa.

Ministan Ilimi Tunji Alausa ya siffanta tsarin a matsayin “babban cigaba”.

“Wannan tsari na Dual Mandate Policy ba gyara ba ne kawai, gagarumin sauyi ne da ke bai wa kwalejojin damar bayar da shaidar NCE da kuma digiri,” in ji ministan kamar yadda sanarwar ta ruwaito.

“Tsarin zai ƙarfafa kwalejojin, ya ƙara yawan damar samun ilimi, kuma ya kyautata ingancin koyarwa a faɗin Najeriya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here