Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu don bai wa ma’aikata damar yin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya.
Ministan Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Bayanin na kunshe cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Laraba a Abuja.
Tunji-Ojo ya yaba wa ma’aikatan Najeriya bisa kwazo da sadaukarwarsu ga ci gaban kasa, yana mai cewa kokarinsu na da matukar muhimmanci ga bunkasa da walwalar Najeriya. Inda ya karfafa ma’aikata da su rungumi kishin kasa, kwazo da sadaukarwa ga aiki. “Wadannan halaye suna da matukar muhimmanci ga ci gaba mai dorewa,” in ji Tunji-Ojo.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kasance mai jajircewa wajen tallafawa jin dadi da tsaron dukkan ma’aikata ta hanyar samar da yanayi mai kyau don bunkasar tattalin arziki.
Ya bukaci ma’aikata da su yi amfani da ranar wajen yin tunani kan muhimmancin hadin kai da aiki tukuru wajen gina kasa.
Tunji-Ojo ya taya ma’aikata a fadin kasar murnar bikin Ranar Ma’aikata na 1 ga Mayu na shekarar 2026 cikin lumana. (NAN)











































