Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS na shirin tattaunawa kan sasantawa da kuma shawo kan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke ƙarƙashin jagorancin mulkin soja daga ficewa daga kungiyar a yayin taron su na gaba kamar yadda gidan rediyon Faransa na RFI ya rawaito.
Ƙasashen uku sun buƙaci gaggauta ficewa daga kungiyar bayan bayyana aniyarsu ta ficewa daga kungiyar a ranar 29 ga watan Janairu.
“Muhimmin ra’ayinmu shi ne a tuntube su don su ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar,” a cewar wata majita.
Karanta wannan: ‘Ƴan Najeriya sun mayarwa da dan shugaban kasa Seyi Tinubu martani
Ta kara da cewa, “Don cimma wannan tattaunawar na iya kasancewa kan takunkumin da aka kakabawa Nijar.”
Shugabannin kasashe irin su Faure Gnassingbe na Togo suna kira da a ɗage waɗannan takunkumin.” Inda ya kara da cewa, “a halin yanzu babu tabbas”.
Rahoton na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka rawaito shugaban hukumar ta ECOWAS Omar Alieu Touray ya ce da wuya ƙungiyar ta baiwa ƙasashen yankin Sahel din uku damar ficewa daga kungiyar da wuri.