Sheikh Gumi yace da gangan Sojoji suka kai hari kan masu Mauludi a Tudun Biri

download (1)
download (1)

Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin cewa da gangan  sojoji suka kai harin bom kan masu taron Mauludi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

Sheikh Ahmad Gumi yace idan har harin bom na farko da jirgin sojan ya kai wa masu Mauludin kuskure ne, to me ya sa bayan minti 30 suka jefa bom na biyun a kan masu aikin ceton wadanda aka jefa wa bom din farko?

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana haka ne a majalisar karatunsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Karanta Wannan:Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bukaci a yi cikakken bincike akan lamarin da ya faru a Jihar Kaduna

Malamin ya ce ko a lokacin yaki ba daidai ba ne a kaiwa mata ko kananan yara ko tsofaffi hari, amma duk da haka sojoji suka kai musu hari, bisa zargin iyalan ’yan ta’adda ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here