Jam’iyyar APC ta ce ta kammala shirin kafa cibiyar samar da ci gaba.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin taron kaddamar da littafin da Dakta Sule Ya’u Sule ya rubuta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa Malam Muhammadu Garba ya ce cibiyar ita ce irinta ta farko a kasar nan.
Yace babban cibiyar shi ne koyarwa da wayar da kan ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki kan samar da ci gaba don karfafa dimokuradiyya.
Ganduje ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya amince da kudirin kafa cibiyar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da littafin na dabarun sadarwa na jama’a, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yaba da nagartar marubucin.
Inda yace Dakta Sule Ya’u Sule kwararren dan jarida ne abin koyi ga ‘yan jarida masu tasowa.
A nasa bangaren, tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya ce dangantakarsa da marubucin ta samo asali ne tun shekaru 20 da suka gabata.
Karanta wannan: Ganduje ya nada sabon shugaban kungiyar Kano Pillars
Shekarau wanda ya ji dadin yadda abubuwa suka wakana a wajen gabatar da littafin ya yaba da hikima, hazaka, hakuri da yadda Sule Ya’u Sule yake gudanar da ayyukansa.
A cewar Shekarau bai taba nadamar dangantakarsa da Dakta Sule Ya’u Sule ba.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Daraktan yada labaransa, Sanusi Bature ya wakilta, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka gabatar da littafin.
Marubucin littafin, Dakta Sule ya ce aikin da ya yi na digirin digirgir da Farfesa Umaru Pate ya duba masa shi ne ya ba shi kwarin gwiwar rubuta wannan littafi saboda akwai karancin adabi a cikin dabarun sadarwa.










































