Jam’iyyar PDP ta kasa ta sake tabbatar da Shehu Sagagi a matsayin shugabanta na Kano

Shehu Wada Sagagi 678x381 1
Shehu Wada Sagagi 678x381 1

Jam’iyyar PDP ta kasa ta bi umarnin kotu inda ta amince da dawo da shuwagabannin jam’iyyar da aka rushe na jihar Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Debo Ologunagba, ya fitar da yammacin ranar litinin.

Sanarwar tace daga yanzu Alhaji Shehu Wada Sagagi da dukkan abokan aikinsa a kowanne mataki za su ci gaba da jagorancin jam’iyyar bayan da aka dawo da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here