Mai Martaba Sarkin Zazzau ya dakatar da Hakimansa 4

Emir of Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli 678x381 1
Emir of Zazzau Ambassador Ahmed Nuhu Bamalli 678x381 1

Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya dakatar da wasu hakimansa 4, jim kadan bayan sauka daga hawan Idi, sakamakon karya dokokin hawan Daba na masarautar.

Wannan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran masarautar Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar a ranar Litinin, inda yace dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

A cewar sanarwar hakiman da aka dakatar sun hadar Uban garin Zazzau kuma hakimin Soba Alhaji Bashir Shehu Idris, da Sarkin Dajin Zazzau kuma hakimin Kubau Alhaji Shehu Umar Aliyu.

Sauran sun hadar da wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da kuma Garkuwan kudun Zazzau Alhaji Muhammad Sani Uwais.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here