Kwamitin zartarwar jam’iyyar APC ta Kasa ya kara wa’adin sayar da takardun nemen tsayawa takara a babban zaben 2023,daga ranar Juma’a 6 ga Watan Mayu zuwa ranar Talata 10 ga watan nan da muke ciki na Mayu.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Jam’iyyar na Kasa Barrister Felix Morka ya fitar a ranar Laraba.
Ta cikin wani jadawali da aka yiwa kwaskwarima mai dauke da sa hannun sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na Kasa Sulaiman Muhammad Argungu, ya nuna cewa ranar Laraba 11 ga watan ita ce ranar karshe ta kamala maida Takardun.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa za a gudanar da tarukan zaben wakilan kananan hukumomi da jihohi da na Tarayya wadanda zasu yi zaben fidda gwanayen ‘Yan takara, a ranakun Alhamis 12 zuwa Asabar !4 ga watan Mayun da muke ciki.













































