Jam’iyyar PDP ta kasa ta gyara Jadawalin tsare-tsarenta na tunkarar Zaben 2023

PDP PDP 1 1
PDP PDP 1 1

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP ta kasa ya kwaskware jadawalin tsare-taren jam’iyyar na tunkarar babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Jam’iyyar ta PDP ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar, mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta Debo Ologunagba, ranar Laraba a Abuja.

A cewar Ologunagba, za a zabi wakili guda tare da wakili mai bukata ta musamman guda shima daga konanan hukumomi 774 na kasar nan, wanda za a gudanar a ranar Talata 10 ga watan nan da muke ciki na Mayu.

Ya kara da cewa za a gudanar da zaben fidda gwanin ‘Yan takarar majalisar dokokin jihohi a ranar 18 ga wata, yayin da na ‘Yan majalisar wakilai zai gudana a ranar 20 ga watan na Mayu, sauran sun hadar da na Majalisar Dattawa da kuma na Gwamnoni a ranakun 21 da 23 ga watan Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here