Mutane 4 ne suka mutu a fashewar Sabon Gari- Rundunar Ƴan sanda

Kano Explosion 678x381 1
Kano Explosion 678x381 1

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane hudu sakamakon fashewar iskar gas da safiyar yau Talata a Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Samaila Dikko, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo da talabijin  yau Talata a Kano.

Dikko ya ce, iskar gas ɗin ta fashe ne a wani wurin walda da ke kusa da wata makarantar firamare da ke kan titin Aba a Sabon Garin Kano.

Haka kuma ƙara da cewa masu aikin ceto na ƙoƙarin gano mutanen da suka makale a cikin ginin da fashewar ta faru.

Dikko ya buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu saboda halin da ake ciki.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, ya bayar da rahoton cewa, fashewar da ta afku a kusa da makarantar Winners Kids Academy ta yi sanadiyar barna a wasu gine-gine na yankin.

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here