Gudaji Kazaure: Majalisa ta Nesanta Kan ta daga Zargin Satar Naira Tiriliyan 89 a CBN 

56e0393009aa3284
56e0393009aa3284

Majalisar wakilan tarayya ta ce ba za ta iya hana Muhammad Gudaji Kazaure aikin binciko zargin badakalar kudi da aka tafka a bankin CBN ba. Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan bayani ne ga manema labarai bayan ya gana da Mai girma shugaban Najeriya a fadar Aso Villa.

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yana ikirarin kwamitinsu ya gano wasu kudi da aka karkatar a bankuna. Fadar shugaban kasa ta musanya zargin nan.

A matsayinsa na shugaban majalisar wakilan tarayya, Gbajabiamila ya ce ba su da hurumi a kan ‘aikin’ da aka ba Kazaure, domin bai shafi majalisa ba.

Rt. Hon. Gbajabiamila yake cewa ‘yan majalisar tarayya za su iya tsoma bakinsu ne idan Kazaure ya yi amfani da karfinsa, ya murkushe ‘yan kwamitinsa.

An rahoto Gbajabiamila yana cewa ba daga majalisar wakilan kasar nan zargin da Gudaji Kazaure yake yi, ya samo asali ba, ya ce wannan ba aikinsu ba ne.

“Babu abin da ya hada wannan da majalisar tarayya. Babu abin da na sani a kai. Ba da matsayar majalisar tarayya aka dogara ba. Ba daga wata tattaunawa a majalisa ya dauko asali ba. Nayi imani ya ce bangaren zartarwa ya ba shi hurumin yin aikin da yake yi.”

”Idan har haka abin yake, babu ruwan majalisar tarayya. Inda kawai majalisa za ta sa baki shi ne idan har ya taba mutucin majalisa.”

Gbajabiamila ya ce da suka tuntubi wasu ‘yan kwamitin da Kazaure yake Sakatare, an fada masu shugaban kasa ya rusa kwamitin ko makamancin haka.

A rahoton Punch, shugaban majalisar ya fadawa manema labarai a ranar Talata cewa nauyin binciken da yake cewa yana yi, yana hannun Kazaure. Garba Shehu ya shaida cewa an ruguza kwamitin nan da ‘Dan majalisar mai wakiltar mazabun Roni, Gwiwa, Yankwashi da Kazaure yake takama da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here