Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Joseph Albasu Kunini, ya yi murabus daga kujerasa kan dalilan kai da kai.
Farfesa Kunini ya sanar da matakin murabus ɗin ne a wata wasika da ya aike wa mambobin majalisar ranar Laraba, kuma mataimakin kakaki, Hammanadama Ibn-Abdullahi wanda ya jagoranci zaman ya karanta.
Shugaban masu ladaftarwa na majalisar, John Kizito Bonzena, wanda ke wakiltar mazaɓar Zing, shi ne mambobin majalisar suka zaɓa a matsayin sabon shugaba ba tare da gardama ba.
Karin bayani nan tafe…….













































