Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji, ya shiga cikin firgici sakamakon kai hare-haren da sojoji suka yi wa ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.
Musa ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) yayin taron lacca na shekara-shekara na NAN ta shirya a Abuja.
CDS Musa ya bayyana cewa kisan da aka yi wa Halilu Buzu da wasu kwamandojin ‘yan ta’adda da dama ya jefa firgici a sansanin Turji da ‘yan kungiyarsa, inda ya ce abin da ya yi na baya-bayan nan alamu ne na firgita.
“Ka ga daga matakin da yake dauka, za ka gane cewa yana cikin fargaba.
“Ya kasance afarko cikin karfin gwiwa yana fitowa yanata surutai da maganganu kamar shi kadai ne ke da iko.
“Yanzu ya san ba shi ne ke rike da tungar dazukan ba. Ya san lokaci ne kawai don Halilu Buzu da aka kashe shi ne ubangidansa.
“Don haka tunda yanzu ya san kwamandan nasa ya tafi, ya san shima yana kan hanya, don haka duk abin da yake yi a yanzu hayaniya ce kawai,” inji shi.
Hukumar ta CDS ta ce tuni dan ta’addan ya sauya maboyar da yake boye kansa.
A cewarsa, rashin tsaro na dadewa saboda talauci, jahilci da rashin shugabanci na gari a wadannan yankuna.
“Yayin da muka fitar da su, da yawa suna tare da su, sannan kar ku manta, muna da iyakar kilomita 1,500 da Jamhuriyar Nijar.
“Muna da wata iyaka da jamhuriyar Benin don haka mutane da yawa ke taruwa a ciki da wajen Najeriya.
“Don haka muna kokarin tabbatar da cewa mun kare wadannan iyakokin don hana su damar shigowa,” in ji shi.
(NAN)













































