Gwamnatin Benue ta kai sumame wajan gyaran motoci mallakin tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom

Samuel Ortom new
Samuel Ortom new

Wani kwamati da sabon gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya kafa domin dawo da kadarorin gwamnati da suka salwanta, a ranar Talata ya kai sumame wajan gyaran motoci wanda mallakin tsohon gwamnan jihar ne, Samuel Ortom a Makurdi.

Ya yin kai sumamen, kwamatin ya kwashe wasu daga cikin motocin da suke wajan, inda wasu suka ki tafiya da kansu, har sai da akai amfanin da wata mota domin jansu.

Ya yin da jam’iyyar PDP ta ke maida martani akan sumamen, ta ce wannan bita da kwalli ne da sabowar gwamnatin kewa tsohon gwamnan.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar ta PDP a jihar, Bemgba Iortyom, ya bayyana kwamatin a matsyin abun kunya.

“Da safiyar yau ne, wasu yan daba da jami’an tsaro ke tafe dasu, suka kai hari wajan gyaran motoci mallakin tsohon gwamnan jihar nan, inda suka dauki wasu motocin dake gurin” Inji sakataren yada labaran PDP.

“Duk da cewa akwai umarnin kotu data hana sabowar gwamnati taba kadarorin tsohon gwamnan.”

A baya bayan nan ne, babban sakataren yada labaran gwamnan jihar ta Benue, Tersoo Kula, ya ce gwamnatin jihar ta lissafa wasu motoci 29 da tsohon gwamnan ya sace.

Kalu a cikin sanarwar daya fitar ya ce tsohowar gwamnatin ta lalata kayan kawata gida, tagogi, kayan wuta da sauran kayan amfanin gidan gwamnatin jihar kafin su gama wa’adinsu.

Inda ya kara da cewa banda guduwa da motoci da yayi wadan da ya hada harda motar kai agajin gaggawa ta asibiti, da kuma motar yan jaridun gidan gwamnati. Inda ya lissafa a kalla motoci 29 wadan da tsohon gwamnan ya sace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here