Barazanar Ambaliya: NEMA ta gana da gwamnonin jihohin kasar nan

Floods in Jigawa
Floods in Jigawa

Babban Darakta na hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, Mustapha Ahmed, ya gana da wasu daga cikin gwamnonin kasar nan a babbar sakatareyar kungiyar gwamonin Najeriya dake Abuja a ranar Talata.

Ganawar na daya daga cikin matakan da hukumar take dauka domin tunkara samun ambaliyar ruwa a bana da ake tsammani.

Bayan kammala taron, Ahamad ya bayyanawa yan jaridu cewa  hadin guwiwa da gwamnonin zai tai maka mutuka wajan rage tasirin ambaliyar ruwan da kuma kare asarar rayuka.

Ya kuma ce yana sa ran gwamnonin zasu ware wasu kudade domin rage raradin ambaliyar idon tazo.

“Gwamnonin na da niyar hada hannun damu, mun musu bayani yacce zasu fahimci illar ambaliyar ruwa, saboda mafiya yawancin su basu gane yadda al’amarin ambaliyar ruwa yake ba, har sai ta faru akan al’ummar su.”

Taron ya samu hallartar gwamnan Kebbi, Anambra, Zamfara, Osun, Cross River da sauransu.

A satin daya gabata gwamnatin tarayya ta bayyana wasu jihohi 14 da garuruwan da zasu iya fuskantar ambaliya ruwa a bana.

Kamar Plateau (Langtang da Shendam); Kano (Sumaila, Tudun Wada); Sokoto (Shagari, Goronyo da Silame); da Delta (Okwe).

Sauran sune Kaduna (Kachia); Akwa Ibom (Upenekang); Adamawa (Mubi, Demsa, Song, Mayo-Belwa, Jimeta, da Yola); da kuma Katsina (Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here