Matashi mai kirkire-kirkire a Kano ya samar da na’urar AI wanda zata gano da kawar da kwarin gona

IMG 20260620 WA0040 675x430

Wani matashi mai kirkire-kirkire dan asalin jihar Kano, Khalifa Aminu ya kirkiri na’urar gonar da ke sarrafa kanta ta hanyar basirar wucin gadi AI da aka tsara domin taimaka wa manoma wajen gano kwarin shuka da kuma fesa magani ta atomatik, wanda hakan ya zama wata babbar nasara a cikin sabbin kirkire-kirkirensa na cikin gida.

Wannan sabuwar kirkira, wadda ke matakin samfuri (prototype) a yanzu, zata iya tafiya cikin gonar da kanta ba tare da mutum ya sarrafa ta ba. Ta amfani da basirar wucin gadi AI, injin yana gane ganyen shuka, yana bincika su don gano alamun kwari, nan take yana fesawa shukar da abin ya shafa maganin kashe kwari.

A cewar Khalifa, injin yana ci gaba da aiki da kansa idan ba a sami kwari ba, hakan yana bai wa manoma damar kula da manyan gonaki cikin sauƙi yayin rage asara daga fesa magani ba tare da tsari ba.

“Wannan injin yana iya tafiya da kansa, yana gane ganye ta amfani da AI, yana bincika su don ganin kwari, kuma yana fesa magani nan take idan ya cancanta. Idan babu kwari, sai ya ci gaba da tafiyarsa,” in ji shi.

Khalifa ya ce aikin har yanzu samfuri ne amma ya bayyana fatan cewa zai iya kaiwa ma’auni na duniya kuma ya samu tallafi don kera shi da yawa.

Wannan kirkira ta kara wa jerin hanyoyin fasaha da matashin mai kirkira ya tsara, wanda ke ci gaba da jawo hankali wajen kirkirar na’urori da nufin magance matsalolin al’umma.

A cikin hirarraki da ya yi da SolaceBase a baya, Khalifa ya bayyana cewa ya kirkiri fasahar AI mai magana da Hausa da ke gano hadari kamar wuta, dibar gas, hayaki, motsi, zafi da sauyin yanayi. Na’urar ta sana bin da ake kira KHALITECH BOT AI, yana yin magana da Hausa kuma ya nuna babban ci gaba wajen haɗa harsunan gida da fasahar zamani.

Matashin mai kirkira ya kuma kirkiri na’ura da ke gano na’urorin fashewa na gida IED da ma’adanai masu karfi a karƙashin kasa cikin takaitaccen lokaci, wata na’ura da ya ce zai iya zama madadin arha na kayan da ake shigowa da su daga waje.

IMG 20260620 WA0041

Kafin wadannan kirkirori, Khalifa ya samu karramawa a matakin kasa saboda kirkirar tabarau (smart glasses) da na’urorin firikwensin da ke taimaka wa makafi wajen guje wa cikas ta hanyar fadakarwa sauti, yana taimaka musu wajen tafiya da kansu cikin aminci.

An haifi Khalifa kuma ya girma a unguwar Gobirawa ta Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, ya koyi ilimin injiniya da fasaha da kansa ta hanyar bincike a intanet, kayan aikin basirar wucin gadi, da gwaje-gwaje. Duk da matsalolin kudi da karatu, ya ci gaba da mai da hankali wajen kirkirar hanyoyin fasaha na cikin gida.

Da sabon injin gonar na AI, Khalifa yanzu yana mai da hankali wajen inganta yawan amfanin gona, yana nuna yadda kirkire-kirkiren gida za su iya ba da gudummawa ga tsaron abinci da zamani a noma a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here