Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta dakatar da gudanar da wasan Tashe na gargajiya a lokacin watan Ramadan domin hana yaɗuwar ayyukan ta’addanci.
An ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da Gwamnatin Jihar.
A al’ada ana gudanar da wasan Tashe ne a rana ta goma a watan Ramadan, inda wasu maza ke sanya abin rufe fuska da tufafin barkwanci suna kwaikwayon abubuwa da mutane a cikin al’umma.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano ranar Lahadi.
Rundunar ta ce ta tanadi matakan tsaro domin daƙile irin waɗannan ayyuka tare da tabbatar da zaman lafiya a lokacin Ramadan.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Bakori, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da kuma al’umma gaba ɗaya da su ba ‘yan sanda haɗin kai tare da hana ‘ya’yansu shiga duk wani abu da zai iya karya doka da oda.
Ya ce duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukunci bisa ga doka.
Rundunar ta kuma yi wa al’ummar Jihar Kano fatan samun nasarar azumin Ramadan.













































