Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya sanar da ayyana zaman makoki na kwanaki 40 da kuma hutun kwanaki bakwai a faɗin ƙasar bayan rasuwar Jagoran Addini, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya shafe shekaru yana mulki tun daga 1989.
Mai gabatar da shirin a gidan talabijin ɗin ya ce, “Da shahadar Jagoran Addini, tafarkinsa da manufofinsa ba za su ɓace ko a manta da su ba; a maimakon haka, za a ci gaba da bin su da ƙwazo da himma.”
Tuni kafafen yaɗa labaran gwamnati suka tabbatar da rasuwar Khamenei, ba tare da yin bayani kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan mazauninsa ba.
Karanta: Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya rasu – Kafafen yaɗa labaran gwamnati
An sanar da rasuwar tasa da misalin ƙarfe 5:00 na safe agogon ƙasar (0130 GMT), yayin da tashar ke nuna hotunan baya tare da saka baƙin tuta a matsayin alamar makoki.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Asabar cewa an kashe Khamenei a hare-haren sama, sai dai babu wani cikakken bayani daga Tehran kan lamarin.












































