Trump zai rage ma’aikatan USAID daga 10,000 zuwa 290 – Rahotanni

Trump USAID 750x430

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa za a rage ma’aikatan hukumar raya kasashe ta Amurka USAID zuwa ma’aikata kadan daga karshen mako.

A cewar jaridar New York Times, gwamnatin Trump na shirin rage ma’aikatan hukumar daga sama da ma’aikata dubu 10,000 a duk duniya zuwa kusan 290, inda ta ambato majiyoyi uku da suka saba da tsare-tsaren.

Gidan Rediyon Jama’a na kasar (NPR) ya ruwaito cewa an gabatar da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da jerin sunayen wasu ma’aikata 600 da ake ganin suna da muhimmanci a duk duniya, amma a karshe an kebe kasa da 300 daga yunkurin rage ma’aikatan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya killace kudaden hukumar a cikin watan Janairu har zuwa wani nazari da zai yi, wanda hakan ya yi tasiri da dimbin tsare-tsare a duniya.

USAID dai na daya daga cikin manyan kungiyoyin bada agaji a duniya kuma ita ce ke da alhakin kashe yawancin taimakon jin kai da gwamnatin Amurka ke yi ga kasashe masu tasowa da kasashe masu fama da rikici.

A wannan makon, gwamnatin Amurka ta sanar da cewa za ta sanya kaso mai yawa na ma’aikatanta ciki hutu daga daren Juma’a.

Karanta: Kotun kolin Amurka ta ki amince yunkurin cire Trump daga zabe

Hukumar da ke karkashin jagorancin Rubio, ta ce za a sanar da wadanda abin ya shafa, kwana daya kafin a dakatar da su.

Kimanin mutane 10,000 ke aiki da hukumar, kashi biyu bisa uku na a wajen Amurka.

A bara, hukumar ta kashe kusan dala biliyan 50 a ayyukan taimakon raya kasa. (dpa/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here