Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sayo sabbin manyan motocin kwashe shara guda 10 da kuma wasu manyan motocin loda sharar guda 3.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a, wannan shiri wani gagarumin yunkuri ne na bunkasa harkokin kwashe da kuma tsaftace muhalli a jihar.
Sanarwar ta ce, sabbin na’urorin na da nufin inganta aikin tattara shara da zubar da ita a fadin jihar, tare da magance kalubalen da aka dade ana fama da su wajen sarrafa shara.
Karanta labari: Zamu kawo karshen zubar da shara ba bisa ka’ida ba a Kano- Kwamishinan muhalli
SolaceBase ta ruwaito cewa, Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi, Dakta Dahir Hashim ne ya gabatar da motocin a hukumance, wanda ya jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da tsaftar muhalli da lafiya.
”Dr. Hashim ya ce, sabbin motocin za su karfafa aikin kwashe shara da sarrafata, har ma da rage gurbatar muhalli, da kuma dakile illolin sauyin yanayi, ”in ji sanarwar.
“Gwamna Yusuf ya nanata kudurin gwamnatinsa na tabbatar da ayyukan muhalli masu dorewa, inda ya bukaci mazauna Kano da su marawa kokarin gwamnati baya ta hanyar kiyaye dabi’ar zubar da shara barkatai.
”Ana sa ran za a tura sabbin injinan nan take zuwa muhimman wuraren da ke fuskantar kalubalen sarrafa shara”.