2023: Za Mu Baiwa Jonathan Damar Tsayawa Takara Idan Ya Dawo Jam’iyar Mu- APC

9010d2eb goodluck jonathan
9010d2eb goodluck jonathan

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 idan ya sauyar sheka zuwa jam’iyyar.

Sakataren Rikon Kwaryar Jam’iyyar APC na Kasa, John Akpanudoedehe, ne ya bayyana hakan a Shirin Siyasa na Gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Ya fadi haka ne lokacin da aka tambaye shi kan hasashe da ake yi na cewa Jonathan na nazarin shiga jam’iyya mai mulki.

Jami’in na APC ya kuma ce tsohon shugaban kasar za a ba shi matsayin Babban memba da aka samar da jam’iyar tare da shi idan ya shiga.

Amma, ya ce damar ba wai za a baiwa Jonathan tikitin takara kaitsaye bane, yana mai cewa zai yi gogayya da sauran membobin jam’iyyar kafin ya samu tikitin.

Karanta Wannan: Lauyoyin Dake Kare Abduljabbar Sun Janye Daga Shari’arsa

Akpanudoedehe ya ce, “A karon farko kenan da nake jin wannan labari da muke tsammanin tsohon Shugaban. Wannan zai zama babban labari. Za mu yi masa maraba; hakan kuma zai karfafa jam’iyyar.

“Kwamitin zartarwar Jamíyar na kasa ya ba da izini ga kowane mutum cewa idan ya shiga APC a yau, kamar membobin da aka kafa jam’iyyar da su ne.

“Don haka, duk wanda ya shiga yau yana da dama iri ɗaya da kowa wajen tsayawa takarar kowane mukami a cikin wannan jam’iyya. Kuma tun-tuni haka ne,”in ji shi.

Karanta Wannan: An Kama Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Kisan Ɗan Sanata Ibn Na’allah

Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare/ Karin-Talakawa na Jam’iyyar All Progressive Congress, Mai Mala Buni, da wasu gwamnonin APC sun sha ziyartar tsohon Shugaban a watan Nuwamba 2020.

Saidai jam’iyyar PDP a wancan lokacin ta karyata rahotannin da ke cewa Jonathan na shirin barin jam’iyyar zuwa APC gabanin zaben 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here