Mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kan harkokin yada labarai Isah Gusau, ya rasu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kwararren a aikin Jarida ya rasu ne a Kasar Indiya sakamakon rashin lafiya.
Karanta wannan: Zulum Ya Hana Gwangwan A Borno
Kafin rasuwarsa ya taba taimakawa mataimakin shigaban kasa Kashim Shettima, ta fuskar yada labarai, lokacin yana gwamnan jihar Borno.
Karanta wannan: NCDC ta aika tawogar ko-ta-kwana zuwa Jigawa, Yobe Katsina a kan cutar sanƙarau
Ya kuma taba kasancewa babban mataimakin Edita, kazalika babban Editan shiyya, baya ga kasancewa shugaban ofishin shiyya, duka a Jaridar Daily Trust.
Muna tafe da Karin bayani nan gaba……












































