An rufe Jami’ar Jihar Tafawa Balewa bayan masu kwacen waya sun kashe wani dalibi

ATBU 1
ATBU 1

Hukumar gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ta rufe makarantar na tsawon mako guda bayan wata zanga-zangar da daliban makarantar suka yi a ranar Litini kan zargin kashe wani dalibin aji 5, Joseph Agabaidu, na tsangayar kimiyya.

Daraktan yada labarai na Jami’ar Zailani Bappah ne ya bayyana haka ga manema labarai a Bauchi.

Zailani, ya tabbatar da mutuwar dalibin inda yace wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka soka wa marigayi Agabaidu wuka a kokarinsu na kwace wayarsa, kuma lamarin ba’a harabar makarantar ya faru ba, ya faru a wajen makarantar ne saboda haka hakkin ‘yan sanda ne su binciki lamarin.

A cewarsa, jami’an tsaron jami’ar sun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Ya ci gaba da cewa an yanke shawarar rufe makarantar ne sakamakon matakin da daliban suka dauka na haifar da rikici a tsakanin al’ummar jami’ar duk da shigar ‘yan sanda lamarin.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaron jami’ar da ‘yan sanda sun yi kokarin dakile zanga-zangar.

Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce duk dalibin da aka samu a harabar jami’ar zai fuskanci fushin doka.

Har kawo lokacin rubuta wannan labari, rundunar ‘yan sandan Jihar ba ta ce komai kan lamarin ba.

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here