Majalisar Dattawa za ta gudanar da bincike kan harin da sojoji suka kai jihar Kaduna

Senate at plenary
Senate at plenary

Majalisar Dattawan Najeriya ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar soji ta kai jihar Kaduna.

Sama da mutane ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu ke kwance a asibiti don kula da lafiyarsu.

Sanata Lawal Adamu Usman, shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, inda aka kai harin, yace wannan batu ne da ba za su bari ya wuce ba haka ba.

Sai dai duk da cewa yanki ne da ke fama tashin hankali sakamakon hare haren ‘yan bindiga amma majalisar dattawan Najeriya ta danganta al’amarin da gazawar sojoji wajen tattara bayanan sirri.

Tunda farko gwmnatin jihar kaduna ta kafa kwamitin bincike kan lamarin.

Ita ma majalisar dattawan kasar ta ce za ta kafa kwamitin binciken akan lamarin tare da kai dauki ga mutanen da ibtila’in ya rutsa da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here