Gbajabiamila ya bukaci jam’iyyun siyasa da su kara himma wajen horar da matasa a tafarkin dimokaradiya

GBAJABIAMILA
GBAJABIAMILA

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bukaci jam’iyyun siyasa da su kara kaimi wajen horas da matasa domin su zama cikin shirin matsayinsu na shugabannin kasar a nan gaba.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne yayin bude taron hadin gwiwa karo na biyu da aka shirya ranar Litinin a Abuja domin horas da matasa 45.

Ya ce za a iya amfani da karfin da matasa ke da shi wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyya a Najeriya ta hanyar ire-iren wadanan shirye-shirye.

Ya kuma bayyana cewa, shirin zai baiwa matasa damar bayar da gudumawa wajen ciyar da Nijeriya gaba.

Gbajabiamila ya kara da cewa: “Wannan zai kara karfafa dimokuradiyyar mu, har ma zai taimaka wajen karfafa jam’iyyun siyasa da kansu da kuma tabbatar da matsayinsu a tsarin dimokuradiyyar mu.”

Gbajabiamila ya ce dole ne a samar da hanyoyin da za’a baiwa matasa masu basira damar shiga fagagen rayuwar al’umma.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Majalisun Dokoki da Dimokaradiyya ta kasa (NILDS) Farfesa Abubakar Sulaiman, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shirin zai ci gaba da bunkasa har ya kai ga wani matsayi.

Suleman ya ce a wani bangare na sadaukar da kai ga wannan shiri, cibiyar NILDS za ta baiwa wadanda suka kwazo cikin mahalartan aikin yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here