Dalilan da suka sanya sojoji suka kai hari Jihar Kaduna-Hedikwatar Tsaro

Chief of Army Staff Lt. Gen. Taoreed Lagbaja
Chief of Army Staff Lt. Gen. Taoreed Lagbaja

Hedikwatar tsaro ta ce harin da jirgin sojoji mara matuki ya kai a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, ya samo asali ne daga wasu bayanai na ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar ranar Talata a Abuja.

Ta cikin sanarwar Buba yace dakarun sojojin Najeriya da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, sun lura da motsin ‘yan ta’adda a yankin Ligarma, wanda aka fi sani da yankin da ‘yan ta’adda suka mamaye a jihar Kaduna.

Ya ce binciken da aka yi ta jirgin sama ya nuna motsin gungun mutane masu kama da dabarun ta’addanci da tsarin tafiyar da su.

A cewarsa, an kawar da wannan barazanar ne domin hana ‘yan ta’addan kai hare-hare kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

A cewarsa, daya daga cikin matakin da sojoji ke dauka shi ne ci gaba da gudanar da ayyukan dakile ta’addanci.

Buba ya ce dakarun sojin kasar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa dokokin kasa sannan za su ci gaba da taka tsantsan da ci gaban da suke samu na kawar da ‘yan ta’adda daga doron kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here