Yanzu-yanzu: Tinubu da Fubara na ganawar sirri a fadar Aso Rock

Rivers Governor Fubara and Tinubu 750x430
Rivers Governor Fubara and Tinubu 750x430

Shugaban kasa Bola Tinubu yana ganawar sirri da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Fubara wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 5:40 na yammacin Alhamis ya wuce ofishin shugaban kasa kai tsaye inda suke ganawar sirri.

Har ya zuwa lokacin gabatar da rahoton ba a san dalilin ziyarar ba.

Karanta wannan: Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana

Wannan ita ce ziyarar farko da Fubara ya kai fadar shugaban kasa tun bayan sanya hannu kan yarjejeniya mai shafi 8 bayan da shugaba Tinubu ya shiga cikin takaddamar da ke tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, wanda kuma shi ne magabacinsa.

Rikicin da ke tsakanin Wike da Fubara ya raba kan ‘yan majalisar dokokin jihar inda 27 daga cikinsu suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A watan Oktoba ne dai shugaban kasar da wasu dattijan kasar suka shiga tsakani a rikicin tun da farko amma abin ya rikide zuwa fada.

Karanta wannan: ‘Yan sanda sun yi fatali da sace matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Da yake nuna damuwa da lamarin, Tinubu ya sake ganawa da ‘yan siyasa a jihar a ranar 18 ga Disambar 2023 kuma an cimma matsaya.

A taron wanda ya samu halartar Fubara da Wike da tsohon gwamnan Rivers Peter Odili, da wasu sarakunan gargajiya daga jihar da kuma mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, an yanke wasu kudirori.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here