Gwamnan jihar kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya aikewa zauran majalisr Kano, sunayen sabbain kwamishinonin da ya nada, domin tantanci su.
Shugaban majalisar, Hamisu Chidari, ne ya karanta wasikar da gwamnan ya aike da ita a yau Litinin.
Sunayen da aka ake dasu sune, Ibrahim Dan’azumi Gwarzo, Abdulhalim Liman Dan Maliki, Lamin Sani Zawiyya, Ya’u Abdullahi Yanshana, Garba Yusif Abubakar, Yusif Jibril Rurum, Adamu Abdu Panda da kuma Saleh Kausani.












































