Kamfanin AEDC ya yi barazanar yankewa fadar Shugaban Kasa wuta

Shugaban Kasa, tinubu, tsadar rayuwa, 'yan kasa, najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri su kuma ci gaba da juriya dangane da halin matsi da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya ba da...

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Abuja AEDC ya yi barazanar katse wutar lantarki a fadar shugaban Najeriya da na wasu ma’aikatun gwamnati 86 a kan bashin kuɗin wuta sama da naira biliyan 47 da yake bin su.

Wasu daga cikin ma’aikatun da barazanar ta shafa sun haɗa da ma’aikatar kuɗi da ta yaɗa labarai da ta kasafin kuɗi da ta ayyuka da gidaje, da gwamnan CBN da kuma ofishin Hukumar EFCC da sauran su.

Karanta wannan: ‘Ƴan bindiga sun kashe mutum 12 da ƙona gidaje a jihar Neja

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, AEDC ɗin ya baiwa ma’aikatu da ofisoshin na gwamnati kwana 10 domin biyan basukan ko kuma a yanke musu lantarki, wato daga 28 ga watan Fabrairun 2024.

Bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya dai ya shafe shekaru yana fama da matsalar bashi.

A makon da ya gabata ne Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ce umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki DisCos da su tashi tsaye idan ba haka ba duk wanda aka samu da laifi za’a soke lasisin sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here