Jami’ar Ilọrin UNILORIN ta kori dalibai 9

Jami'ar Ilorin, UNILORIN, dalibai, kori
An kori dalibai 9 ciki har da 4 da suka kammala karatu a matakin karshe na jami’ar Ilọrin UNILORIN da ke jihar Kwara, bisa zarginsu da tafka magudin...

An kori dalibai 9 ciki har da 4 da suka kammala karatu a matakin karshe na jami’ar Ilọrin UNILORIN da ke jihar Kwara, bisa zarginsu da tafka magudin jarrabawa.

Wannan na kunshe ne a cikin bayanan jami’ar da aka fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce korar daliban ya biyo bayan shawarwarin kwamitin ladabtar da daliban ne a taronta na 219 wanda mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Wahab Egbewole ya amince da shi.

Karanta wannan: Kamfanin AEDC ya yi barazanar yankewa fadar Shugaban Kasa wuta

Ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da Lateef Lukman Olayemi dalibi a matakin 500 da Kuranga Abdulmuiz Olalekan dalibi mai mataki 500 da Adebisi Janet Bosede dalibi mai mataki 100 da Ogundijo Abdulmalik Akinkunmi na mataki 500 da kuma Ashekun Oladiji Quadri mai mataki na 400 a Kimiyyar Sadarwa.

Sauran sun hada da Eqwudah Lucky Ojonumba mai matakin 300 da Musa Mohammed Asuku mai matakin 500 da Ahmed Saddam Opeyem mai matakin 500 tare da Ayinla Jamiu Olaitan na Kimiyyar Rayuwa a mataki na 400.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here